25 Agusta 2025 - 16:54
Source: ABNA24
Hizbullah Da Amal Sun Yi Kira Da A Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Hukuncin Da Gwamnati Ta Yanke

Sanarwar da kungiyar Hizbullah da ta Amal ta fitar ita ce kamar haka: Ya ku ma'aikata da masu kere-kere na kasar Labanon, hakurin da muke da shi kan kalubalen da kasarmu ke fuskanta ya tsawaita, kuma lokaci ya yi da za mu bayyana matsayinmu na kasa guda daya Muna gab da tsayawa tsayin daka na kasa don nuna kin amincewa da tsarin mika wuya da sallamawa, da kuma kare karfi da ikon kasar Lebanon".

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya kawo cewa: ofishin kula da harkokin kwadago na kungiyar Amal da na kungiyar kwadago da ma’aikatan kungiyar Hizbullah a cikin wata sanarwa da suka fitar, sun yi kira ga ma’aikata, furodusoshi, da ‘yan kungiyar masu daraja na kasar Lebanon da su hallara a dandalin Riyadus-Solh a ranar Laraba 27 ga watan Agusta, 2025, da karfe 5:30 na rana, don nuna kin amincewa da hukuncin da gwamnatin kasar ta bayar a ranar 7 ga watan Agusta. 2025, wanda ya saba wa babban muradin kasa, daftarin yarjejeniyar kasa, da tsarin zaman tare da tabbatar da 'yancin kasar Labanon na kiyaye 'yancinta da 'yancin al'ummarta da tsayin daka wajen kare kasarsu da 'yantar da ita daga mamayar "Isra'ila" da nuna imani ga tsarkin gwagwarmaya da makamanta masu daraja da ke kare kasar, da kokarinta wajen kare hukunce-hukuncen Lebanon daga duk wani matsin lamba na waje, zanga-zangar zata gudna karkashin taken "Ba Zamu Dauki Kaskanci Ba" sanarwar ta kara da cewa, "Ya ku ma'aikata da furodusoshi na kasar Labanon, hakurin da muke da shi kan kalubalen da kasarmu ke fuskanta ya tsawaita, kuma lokaci ya yi da za mu bayyana matsayinmu na kasa baki daya’ Muna kan hanyar da za ta bi wajen nuna kin amincewa da tsarin mika wuya da sallamawa, da kuma kare karfi da ikon kasar Lebanon".

Sanarwar ta kara da cewa, wannan matsayar na tabbatar da hakkinmu ne na kiyaye makamanmu, wadanda suka tabbatar da karfinsu na karya kashin bayan makiyanmu, da kuma hakkinmu na tinkarar makiya "Isra'ila" da suke keta kasarmu, suna masu mamaye wani bangare na kasar, da kuma tauye 'yancinmu.

Ta kara da cewa: “Fitowarmu kuma zata tabbatar cika alkawarinmu ga jinin shahidanmu salihai, da kuma imani da abin da muka koya daga Imam Boyayyen Sayyid Musas-Sadr cewa: “Isra’ila babbar Sharri, kuma mu’amala da ita haramun ce, da fadar Imam Khumaini, Qs da ke cewa: ‘‘Isra’ila saiwar cutar kansa ce”.

Daga karshe: "Ya ku ma'aikata da furodusoshi na kasar Labanon, ya ku 'yan kungiyar hadin gwiwa, ranar Laraba 27 ga Agusta, 2025, ta kasance ranar da tarihi zai dawwamar a tarihin gwagwarmayar ku, tare da kasantuwar ku da kukan ku da ke tabbatar da ku dagewa da yin watsi da duk wani mika wuya. Wannan matsaya na nuni ne da matsayin tsayin daka da kare martabar al'ummarta".

.................

Your Comment

You are replying to: .
captcha